Kofar Sin a bude take game da hadin gwiwa da Amurka a fannin binciken samaniya
2024-06-06 20:15:17 CMG Hausa
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce har kullum kofar Sin a bude take game da fatanta na yin hadin gwiwa da kasar Amurka a fannin binciken sararin samaniya.
Mao Ning, ta bayyana hakan ne a Alhamis din nan, yayin taron manema labarai na rana-rana da ta jagoranta, bayan da a jiya Laraba, babban jami’in hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka NASA, mista Bill Nelson, ya gabatar da sakonsa na taya murnar nasarar da Sin ta samu, ta harba na’urar binciken duniyar wata ta Chang'e-6. Mista Nelson ya bayyana fatansa na kara fadada tattaunawa, da hadin gwiwa da bangaren Sin a fannin binciken samaniya.
A cewar jami’ar, Sin na fatan bangaren Amurka zai aiwatar da matakai na hakika, wadanda za su kawar da duk wani shinge da ka iya yin tarnaki ga hadin gwiwar sassan biyu a wannan fanni.
Mao Ning ta kara da cewa, a halin da ake ciki, akwai wasu matsaloli, da wahalhalu da ake fuskanta a fannin hadin gwiwar Sin da Amurka ta fuskar binciken samaniya, wadanda kuma tushensu shi ne dokokin cikin gida na Amurka, irinsu “Wolf Amendment”, wadda ta yi karan tsaye ga gudanar da musaya, da tattaunawa tsakanin hukumomin lura da ayyukan binciken sararin samaniya na kasashen biyu.
Ta ce, idan har da gaske Amurka na da burin ingiza musaya, da hadin gwiwa tsakaninta da Sin a fannin binciken samaniya, to, ya zama wajibi ta aiwatar da matakai na zahiri, na kawar da wadancan shingaye". (Saminu Alhassan)