Sudan da Sudan ta kudu na tattauna yiwuwar ci gaba da safarar danyen mai
2024-06-03 09:42:29 CMG Hausa
Shugaban gwamnatin rikon kwarya ta kasar Sudan Abdel Fattah Al-Burhan, ya tattauna da mashawarcin shugaban Sudan ta kudu a fannin tsaron kasa Tut Gatluak, game da yiwuwar sake ci gaba da safarar danyen mai mallakin Sudan ta kudu ta iyakokin Sudan.
Wata sanarwa da aka fitar, ta rawaito mista Gatluak na cewa yayin tattaunawar ta jiya Lahadi, an amince da kiran taron ministocin mai na kasashen biyu, domin tattauna yadda za a shawo kan matsaloli masu nasaba da batun safarar danyen man.
Kaza lika, sanarwar ta ce Gatluak ya mika rubutaccen sakon shugaban Sudan ta kudu Salva Kiir Mayardit, don gane da bunkasa dangantaka tsakanin sassan biyu.
A watan Maris da ya gabata ne gwamnatin Sudan ta sanar da dakatar da damar da Sudan ta kudu ke amfani da ita, ta safarar danyen mai ta kan iyakokin kasar Sudan, saboda matsalar da ta ce an samu a hanyoyin safarar man. (Saminu Alhassan)