An kaddamar da sabuwar hedikwatar hukumar tattara bayanan sirrin harkokin tsaro ta Najeriya a birnin Abuja
2024-05-31 09:17:55 CMG Hausa
An kaddamar da sabuwar hedikwatar hukumar tattara bayanan sirrin harkokin tsaro ta Najeriya a birnin Abuja.
A lokacin da yake bude ofishin jiya Alhamis 30 a madadin shugaba Bola Ahmed Tinubu, shugaban majalissar dattawan kasar Sanata Godswill Akpabio ya tabbatar da cewa, a shirye Najeriya take wajen tabbatar da ganin ta samu galaba a kan makiya dake kawo cikas ga zaman lafiyar kasar.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Shugaban majalissar dattawan ta Najeriya a madadin shugaban kasa ya ce, gwamnati tana alfahari da namijin kokarin dakarun sojin Najeriya da hukumomin leken asiri na kasar wajen shawo kan munanan ayyukan masu tada kayar baya a kasar da kuma hare-haren ’yan ta’adda.
Shugaban na Najeriya ya ce, ba ya wasa wajen ganin cewa kowanne bangare na kasar yana cikin yanayin tsaro ingantacce.
Ya ce, hukumar tattara bayanin sirri na tsaro ta kasa, hukuma ce mai matukar muhimmanci ga rundunar soji da kuma ma’aikatar tsaro ta kasa wajen samun nasarar ayyukansu.
Shugaban na tarayyar Najeriya ya ce, ganin yadda kasar ke fuskantar barazanar tsaro daga ’yan ta’adda, ya sanya gwamnati inganta tsarin aikin hukumar ta hanyar samar da na’urorin aiki na zamani da za su baiwa sojoji damar amfani da dabarun sirri wajen gano duk wani motsi na ’yan ta’adda a duk inda suke a kasar.
Shugaban ya kara jaddada kudirinsa na ci gaba da bayar da kulawa ta fuskar horo ga dakarun sojin kasar da samar musu da kayayyakin aikin da suke bukata tare da kula da walwalarsu domin cimma bukatun da ake nema.
“Na yi imani cewa ta amfani da abubuwan dake kunshe cikin wannan katafaren gini za ku fito da sabbin dabarun fasahar tattara bayanan sirri da za su baiwa Najeriya nasara a kan abokan gaba domin dai samun kwanciyar hankali a kasa.” (Garba Abdullahi Bagwai)