logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara daukar matakan saukaka farashin gidaje a kasar

2024-05-27 09:51:04 CMG Hausa

Ministan gidaje da raya birane na tarayyar Najeriya Architect Ahmed Musa Dangiwa ya jaddada kudurin gwamnatin kasar wajen kawo tsafta a hada-hadar kasuwannin gidaje da filaye da zumma tabbatar da ganin kowane dan kasar yana rayuwa cikin yanayin muhalli mai inganci.

Ministan ya tabbatar da hakan ne a karshen mako yayin taron manema labarai da ma’aikatar yada labarai ta saba shiryawa shugabannin ma’aikatu da hukumomin gwamnati a birnin Abuja, ya ce gwamnati za ta gina gidaje masu saukin kudi har dubu 50, kuma za a yi aikin ne kashi-kashi.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

 

Ministan ya ce, kaddamar da shirin bunkasa birane da unguwanni da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a cikin wannan shekarar a yankin gundumar Karsana dake Abuja karkashin shirinsa na sabunta fata ga makomar kasa zai bayar da damar samar da rukunin gidaje dubu 50 a sassan kasar daban daban.

Architect Ahmed Musa ya ce, gwamnati ta tsara gina kananan birane ta hanyar samar da gidaje guda dubu daya a wuri guda a shiyoyi 6 dake kasar, ciki har da birnin Abuja, sai kuma rukunin unguwanni  da za a gina gidaje dari 5 inda kowacce jiha za ta ci gajiya, kuma gwamnati ta yi la’akari ta karfin aljihun kowane dan kasa wajen tsara ginin gidajen.

“Akwai gida mai daki daya, akwai mai daki biyu, kana da masu dakuna uku har zuwa biyar sai kuma tsarin benaye wanda dukkansu an katange, sannan kuma kowane daki akwai damar a kara fadada shi zuwa dakuna biyu.”

Ministan ya tabbatar da cewa, gidajen da aka gina karkashin shirin sabunta fata na gwamnatin shugaba Tinubu za a yi kasuwancinsu ne, amma za a sayar da kaso mafi tsoka bisa farashi mai ragwame ga mutane masu karamin karfi da matsakanta wanda ke cikin kungiyar kodagon kasar.

Ya ce babu shakka aikin ginin gidajen zai samar da guraben aiki na kai tsaye har guda miliyan daya da dubu dari biyu da hamsin, baya ga bunkasa hada-hadar kasuwancin kayayyakin gine-gine da sauran sana’o’i a wuraren da za a gudanar da ayyukan. (Garba Abdullahi Bagwai)