logo

HAUSA

UNICEF ta gyara wasu kananan cibiyoyin kiwon lafiya a Derna na kasar Libya

2024-05-20 10:57:52 CMG Hausa

Asusun kananan yara na MDD UNICEF, da hadin gwiwar kungiyar tallafawa ayyukan jin kai ta kasa da kasa ko “International Medical Corps” reshen kasar Libya, sun gyara wasu kananan cibiyoyin kiwon lafiya dake birnin Derna na gabashin kasar Libya, bayan da ambaliyar ruwa ta lalata su a shekarar da ta gabata.

Wata sanarwa da UNICEF din ya fitar a jiya Lahadi, ta ce cibiyoyin da aka gyara sun hada da na Derna-Alfateeah, da Albomba, da Ras Alteen da kuma Lathron.

Ayyukan da aka gudanar domin daga matsayin ingancin cibiyoyin a cewar sanarwar, sun hada da sanya kofofi, da tagogi, da ayyukan lantarki, da sanya fitilu. Kaza lika, an dawo da muhimman hidimomi da a baya suka daina aiki a cibiyoyin.

Bayan kammala gyaran, sanarwar ta ce yanzu kimamin mutane 10,000, ciki har da yara kanana 4,300, na cin gajiyar ingantattun kayayyakin kiwon lafiya, wanda hakan ke tabbatar da kyakkyawan sakamako a fannin kula da lafiya, da karin ingancin rayuwar al’ummun wurin. (Saminu Alhassan)