logo

HAUSA

OCHA na kara kaimin shawo kan annobar kwalara a Somalia

2024-05-20 11:49:13 CMG Hausa

Ofishin tsare tsaren ayyukan jin kai na MDD ko OCHA, ya ce yana kara zage damtse wajen shawo kan annobar amai da gudawa, ko kwalara da ta barke a wasu sassan kasar Somalia, wadda daga watan Janairu zuwa yanzu ta hallaka kimanin mutane 120.

Rahoton da ofishin na OCHA ya fitar jiya Lahadi a birnin Mogadishu fadar mulkin kasar, ya ce an samu sabbin wadanda suka harbu da cutar har mutum 10,647 daga sassan jahohi 7 na kasar, inda kuma kiyasin kisan da annobar ta yi ya kai kaso 1.1 bisa dari. OCHA ya ce akwai bukatar gaggauta samar da karin kudade, domin tallafawa al’ummun da annobar ta shafa.

A daya bangaren kuma, ofishin na OCHA ya ce ruwan sama kamar da baki kwarya dake ci gaba da sauka na iya ingiza yaduwar annobar, wadda tuni ta yi matukar yaduwa a wasu wurare. Adadin mizanin kisan da cutar ta kwalara ke yi ya dan haura matakin gaggawa na hukumar lafiya ta duniya WHO, wanda ya dan gaza kaso 1, ko ya kai kaso 1.

Ofishin na MDD ya alakanta bazuwar annobar a Somalia da karuwar yawan mutane, da rashi samun tsaftacaccen ruwan sha da tsaftar muhalli.  (Saminu Alhassan)