logo

HAUSA

Ministocin harkokin wajen kasashen AES sun gabatar da rahoton karshen taronsu ga shugaban kasar Nijar

2024-05-19 14:40:22 CMG Hausa

Shugaban kwamitin ceton kasa na CNSP, shugaban kasa, birgadiye-janar Abdourahamane Tiani ya gana a ranar 17 ga watan Mayun shekarar 2024 da ministocin harkokin wajen kasashen yankin Sahel na AES a fadar shugaban kasa dake birnin Yamai. 

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

Su ne, Abdoulaye Diop na kasar Mali, da Karamako Jean Marie Traore na kasar Burkina Faso da kuma takwaransu na kasar Nijar Bakary Yaou Sangare.

Tattaunawar ta gudana a gaban idon faraministan kasar Nijar Ali Mahamane Lamine Zeine da sauran mambobin gwamnati da na kwamitin ceton kasa na CNSP.

A karshen wannan haduwa, ministan harkokin wajen kasar Mali Abdoulaye Diop ya bayyana cewa, sun zo domin yiwa shugaban Nijar godiya bisa ga ayyukan da kasar Nijar ta shirya domin baiwa ministocin harkokin wajen kungiyar kasashen yankin Sahel na AES damar kasancewa a nan birnin Yamai domin shimfida karin ginshikan bukatun al’umomin kasashen AES, har ma da na shugabannin kasashen uku na tabbatar da aiwatar da niyyar cimma wata hadakar siyasa, tattalin arziki da ta soja, ta yadda za’a kara zurfafa wadannan ginshikai. Muna iyar a yau, bayan gabatar da rahoton karshen taronmu ga birgadiye janar Abdourahamane Tiani, mu gaya masa karara cewa an yanke cibiyar wannan hadaka. Babban aikin da ya rage shi ne tabbatar da sauran ayyuka domin soma aikin wannan gamayya, in ji Abdoulaye Diop.

Ministan harkokin wajen kasar Mali, ya kara da cewa, sun fito daga wannan ganawa tare da shugaban kasar Nijar cike da kuzari da imanin kara jaddada goyon bayansu ga kasar Nijar da al’ummarta, ga kuma al’umomin kasashen yankin Sahel na AES da suka hada da Mali, Nijar da Burkina Faso bisa kokarinsu na fuskantar kalubalen ta’addanci da na neman a wargaza su.

Mamane Ada, sashen Hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.