logo

HAUSA

Firaministan Habasha ya kaddamar da asibitin sojoji na kasar da ya samu tallafin Sin

2024-05-19 15:34:49 CMG Hausa

Firaministan Habasha Abiy Ahmed, ya kaddamar da asibitin sojoji na kasar dake garin Bishoftu na jihar Oromia, a jiya Asabar.

Ana ganin sabon asibitin wanda kasar Sin ta samarwa tallafin kayayyakin lafiya tare da horar da ma’aikatansa, a matsayin mafi inganci cikin asibitocin kasar.

Yayin kaddamarwar, Abiy Ahmed ya bayyana asibitin a matsayin na musammam, bisa la’akari da kayayyakin kiwon lafiya masu inganci dake amfani da fasahohin zamani da yake da su.

Ya ce asibitin zai samar da hidimomin kiwon lafiya masu inganci da a baya ake ganin ba za a iya samu a cikin kasar ba. (Fa’iza Mustapha)