logo

HAUSA

An gudanar da taron dandalin hadin gwiwar Sin da Zambiya kan neman ci gaba mai inganci

2024-05-17 14:27:12 CMG Hausa

An gudanar da taron dandalin hadin gwiwar Sin da Zambiya kan neman ci gaba mai inganci, a ranar Laraba a birnin Lusaka fadar mulkin kasar Zambiya. Wakilai fiye da 1000 daga sassa daban-daban na kasashen biyu, sun halarci taron domin tattaunawa kan abokantaka, da hadin gwiwa, da kuma cimma makoma a nan gaba.

Shugaban kasar Zambiya Hakainde Hichilema, da ministocin kasarsa 18 ne suka halarci taron. Kuma shugaba Hichilema, ya bayyana fatan cewa, 'yan kasuwa na kasashen biyu za su yi amfani da wannan dandali yadda ya kamata, tare da yin nazari sosai kan damar yin hadin gwiwa.

Ya ce Zambiya na fatan ganin shigar karin jari daga kasar Sin, don taimakawa kasar wajen karfafa masana'antu, da samar da karin ayyukan yi, da samar da guraben kasuwanci ga matasan Zambiya.

A nasa bangare, jakadan kasar Sin dake Zambia Du Xiaohui, cewa ya yi wannan dandali wani muhimmin lamari ne na aiwatar da ra'ayin bai daya, wanda shugabannin kasashen biyu suka cimma, da murnar cika shekaru 60 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Zambiya, da kuma neman cimma nasarar shirya bikin shekarar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu. Kaza lika wani muhimmin sashe ne na share fagen sabon taron dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afirka.

A yayin taron, kamfanonin Sin da na Zambiya, sun daddale takardun hadin kai guda 21, wadanda suka shafi makamashi, da ma’adinai, da ababen more rayuwa, da aikin gona da dai sauransu. (Bilkisu Xin)