logo

HAUSA

Jakadan Sin: Mu’ammala tsakanin kafofin watsa labarai ta ilmantar da Sudan ta Kudu

2024-05-16 14:20:31 CMG Hausa

Jakadan kasar Sin a Sudan ta Kudu Ma Qiang, ya bayyana jiya Laraba cewa, mu’ammala tsakanin kafofin watsa labarai na kasashen biyu, ta inganta, da karfafa dangantakar al’adu ta hanyar ilmantar da al’ummun Sudan ta Kudu.

Jakada Ma, ya bayyana hakan ne a gun taron tattaunawa na kafofin watsa labarai da aka gudanar a Juba, babban birnin kasar. Ya ce mu’ammalar kafofin watsa labarai ta tsawon shekaru masu yawa, ta inganta mu’ammalar al’adun kasashen biyu.

Jami’in ya kara da cewa, kafofin watsa labarai, muhimman dandaloli ne dake karfafa fahimtar juna tsakanin kasashen Sin da Sudan ta Kudu. Kaza lika, karkashin gudummawar kafofin, al’ummun Sin na iya ganin kasar Sudan ta Kudu, wadda ke neman samun zaman lafiya da kwanciyar hankali, kuma mai cike da damar samun ci gaba.

‘Yan jarida da editoci na kasar Sudan ta Kudu 15, sun halarci taron tattaunawar na kafofin watsa labarai. (Safiyah Ma)