logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta musanta zargin cewa tana shirin samarwa sojojin kasashen waje sansani a kasar

2024-05-08 10:23:35 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta musanta zargin cewa tana shirin baiwa sojojin kasashen wajen sansani a cikin kasar.

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasar Alhaji Muhammad Idris ne ya bayyana hakan ranar 6 ga wata a birnin Abuja yayin wata hira da manema labarai, ya ce mikiya ne kawai ke yada wannan jita-jita.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Ministan yada labaran ya bukaci al’ummar kasar da su yi watsi da wannan furofaganda da wasu tsiraru ke yadawa domin haifarwa gwamnati fitina a cikin kasa.

Ya ce ko kadan dai gwamnati ba ta taba wani yunkuri ba na tattaunawa da wata kasa domin ta jibge sojojinta a Najeriya, haka kuma babu wata kasa da ta tunkari Najeriya da irin wannan bukata.

“Ko da yake kowa ya san dai muna da alaka ta aikin hadin gwiwa da wasu kasashen ketare domin yaki da matsalolin tsaro a cikin kasa, kuma za mu ci gaba da karfafa wannan alaka, amma dai babu wani batu na samar da sansanin sojin kasashen waje a nan Najeriya.”

A dai ranar 3 ga wannan watan ne dattawan arewacin Najeriya suka aikewa shugaban kasar da kuma shugabannin majalissun dokokin kasar wasikar dake kiran da su yi watsi da matsin lambar kasashen Amurka da Faransa na neman a ba su sansanin da za su jibge dakarunsu a Najeriya. (Garba Abdullahi Bagwai)