logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Zamfara za ta sake mayar da dakarun soji yankin Zurmi domin tabbatar da tsaro

2024-05-06 17:02:52 CMG Hausa

Gwamnatin jihar Zamfara a arewacin Najeriya ta tabbatar da cewa, za ta sake tura dakarun tsaron soji zuwa yankuna ukun da ’yan bindiga suka kai hari kwanakin baya a yankin karamar hukumar Zurmi.

Kwamishinan ayyukan na musamman na jihar Alhaji Naziru Zurmi ne ya tabbatar da hakan a karshen mako lokacin rabon kayan tallafi ga mutanen da suka rasa mahullansu yayin harin. Kwamashinan yana tare ne da shugaban majalissar dokokin jihar Alhaji Bilyaminu Moriki.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

A yayin harin da ’yan bindigar suka kai garuruwan gidan dan Zara gabas da Boko haruguji da kuma Zurmi sun kona gidaje da dama tare da shaguna da kuma dakunan ajiyar abinci, haka kuma sun yi garkuwa da wasu mutane da dama dake garuruwa.

Kwamishinan ya ce, a baya yankin ya kasance cikin zaman lafiya bayan samun nasarar yakar ’yan bindigar da suka yi sansani a yankin, amma harin na baya bayan nan ya tilastawa gwamnati sake daukar wani sabon mataki.

“A namu bangaren za mu yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da ganin wannan abu bai sake faruwa ba, haka kuma za mu tabbatar da tura dakarun tsaro masu yawa zuwa yankunan da hare-haren suka faru.”

Kwamishinan ya kara jaddada kudurin gwamnati na ceto mutanen da aka yi garkuwa da su cikin gaggawa.

A jawabinsa shugaban majalissar dokokin jihar ta Zamfara wanda shi ne ya jagoranci tawagar da suka kai kayan agajin zuwa sansanin da aka tsugunar da mutanen da harin ya shafa, ya ce babu shakka gwamnati ta kadu sosai da samun wannan labari.

“Tun farko faruwar al’amarin mun fara kawo ziyarar jaje ne, yanzu kuma muka sake dawowa domin gabatar da wannan tallafi da suka kunshi Masara da Shinkafa domin dai a saukakawa mutanen.” (Garba Abdullahi Bagwai)