Za A Watsa Shirin “Labarun Da Xi Jinping Ya Fi So” A Manyan Kafofin Watsa Labaru Na Wasu Kasashe
2024-05-05 16:20:22 CMG Hausa
A yayin ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi jinping zai kai kasar Serbia, za a watsa shirin bidiyo na “Labarun da Xi Jinping ya fi so” da babban rukunin gidajen radiyo da talabijin na kasar Sin CMG ya shirya musamman domin masu kallo na ketare a babban gidan radiyo da talibijin na kasar a ranar 8 ga wata bisa agogon wurin. Tun daga jiya Asabar kuma, aka fara watsa dandano da faifan bidiyon tallar a manyan kafofin watsa labarai na wasu kasashe, ciki har Serbia, da jamhuriyar Montenegro, da Bosnia da Herzegovina da dai sauransu.
Shirin “Labarun da Xi Jinping ya fi so” na maida hankali kan wasu batutuwan da suka shafi samun wadata tare, da kiyaye muhallin hallitu da dai sauransu, wanda kuma ya kunshi jerin zababbun labarai da kalamai da shugaba Xi ya ambata a cikin muhimman jawabai, da rubuce-rubucen da ya gabatar, wadanda suka bayyana hikimar siyasa da zurfin ilimin tarihi da na al’adu na shugaba Xi, tare da yin bayani mai zurfi game da ma’ana da dabi’u na gama-gari wadanda ke kunshe cikin kyawawan al’adun Sinawa. (Mai fassara: Bilkisu Xin)