logo

HAUSA

Kamfanin Sin ya bayar da tallafin kayayyaki ga wadanda ambaliya ta shafa a Kenya

2024-05-01 20:28:50 CMG Hausa

Kamfanin gine-ginen tituna da gadoji na kasar Sin CRBC, ya bayar da gudunmuwar kayayyakin rayuwar yau da kullum ga daya daga cikin mafaka mafi girma ta wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Nairobin Kenya.

An gudanar da bikin mika kayayyakin ne jiya Talata a makarantar MCEDO-Beijing, wadda ke tsakiyar unguwar Mathare, da kamfanonin Sin suka tallafa wajen gina ta. Manyan ma’aikatan CRBC da malamai da dalibai da iyaye, duk sun halarci bikin.

Kamfanin CRBC mai gudanar da manyan ayyukan more rayuwa a kasar ta gabashin Afrika, ya bayar da gudunmuwar da ta kunshi buhunan garin masara 2,500 da barguna 1,000 da gorunan ruwa 2,500 da buhunan suga 2,500 da kuma kwalaban man girki 2,500. (Fa’iza Mustapha)