logo

HAUSA

FIFA ta gargadi Kenya game da yiwuwar fuskantar wani sabon mataki na dakatarwa sakamakon dage taron AGM

2024-04-04 20:11:11 CMG Hausa

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta ja kunnen kasar Kenya, gane da yiwuwar fuskantar matakin dakatarwa daga shiga wasannin kasa da kasa, idan har kasar ta hana gudanar da babban taron hukumar kwallon kafar kasar na shekara shekara ko AGM.

Wannan gargadi dai na zuwa ne, bayan da sakataren hukumar kwallon kafar kasar FKF mista Barry Otieno, ya aikewa FIFA wasikar korafi, yana mai sanar da hukumar cewa wata babbar kotun kasar dake birnin Mombasa, ta ba da umarnin dage gudanar da taron na AGM, wanda aka tsara gudanarwa a ranar 16 ga watan Maris a birnin Nairobi.

Kafin umarnin kotun, wakilan hukumar FKF su 76, daga sassan kasar daban daban sun hallara a Nairobi, domin tattaunawa kan muhimman batutuwa da suka hada da sanya ranar zaben wakilan FKF, wanda ake fatan gudanarwa a watan Oktoban shekara mai zuwa, sai dai kwana guda kafin shiga taron, kotun ta bayar da umarnin dage zaman.

Sakamakon wasikar koke da ya gabatarwa FIFA, mai dauke da kwanan wata 26 ga watan Maris, wadda kuma jami’in cudanyar hukumomi na FIFA Kenny Jean Marie ya sanyawa hannu, kuma kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya ga kwafin ta, FIFA ta gargadi Kenya da ta kaucewa matakan da za su haifar da sanya mata takunkumi, bisa abun da FIFAn ta kira tsoma hannun gwamnati cikin harkokin kwallon kafan kasar.

A cewar FIFA, umarnin da waccan kotu ta bayar, ya sabawa sashe na 69 na dokokin gudanar da hukumar FKF, wanda ya nuna cewa ba wata kotun kasa dake da hurumin shiga batun warware rashin fahimta a fannin kwallon kafa ba, wanda kuma hakan ya dace da dokokin hukumar FIFA da takwararta ta Afirka CAF.

Cikin wasikar koken ta mista Barry Otieno, ya ce "Mun damu matuka da jin labarin umarnin kotu, wanda ya tilasa dage wannan babban taro na hukumar FKF, umarnin da ya zo mana kwana guda kafin fara taron. Muna son kara bayyana cewa, hakan keta hurumin jagoranci, da ma na mambobin FKF ne, kamar yadda hakan ke bayyane cikin dokokin FIFA, kuma hakan na iya haifar da kakaba takunkumi”.

Labarin wannan danbarwa dai ya zo ne ‘yan sa’o’i kalilan, bayan da kungiyar kwallon kafa ajin maza ta kasar Kenya, wato Harambee Stars ta yi nasarar lashe gasar kasashe 4 da aka kammala a kasar Malawi, bayan da ta doke Zimbabwe da 3 da 1, a wasan karshe da aka buga ranar Talatar makon jiya.

Tun da farko wani mai fashin baki a harkokin wasanni mazaunin Amurka ne ya garzaya kotu, yana bukatar kotun ta dakatar da taron na FKF, bisa zargin cewa wakilan da za su halarci taron ba su cika ka’idar zama mambobin FKF din ba.

Bayan karbar korafin, kotun ta sanya ranar 18 ga watan Maris domin sauraron kasar, ko da yake hukumar FIFA ta ce za ta sanyawa kasar ta Kenya takunkumi, ba tare da la’akari da sakamakon hukuncin da kotun za ta yanke ba.

A baya ma, a watan Fabarairun shekarar 2022, FIFA ta dakatar da Kenya daga buga wasannin kasa da kasa, bayan da gwamnatin kasar ta sauya shugaban hukumar FKF Nick Mwendwa, sakamakon zarginsa da aikata wasu laifuka masu nasaba da cin hanci, kafin daga bisani a mayar da shi kujerarsa a watan Nuwamban shekarar ta 2022. A wancan karo, dakatarwar da FIFA ta yiwa Kenya, ta sanya kasar rasa damar buga gasar kwallon kafa da hukumar AFCON ta nahiyar Afirka ta shirya a shekarar 2023.

A wannan karo ma ana ganin idan har FIFA ta sanyawa Kenya takunkumi, hakan zai hana kasar damar buga gasar AFCON ta 2025, da kuma damar buga gasar cin kofin duniya ta FIFA ta 2026, wadda za a fara buga wasannin fidda zakarun ta daga watan Yunin dake tafe.