logo

HAUSA

Kila yin amfani da kayan laturoni na zamani fiye da yadda ake bukata a lokacin yarantaka zai yi illa ga karatu

2023-06-06 08:08:19 CMG Hausa

 

Masu nazari sun gano cewa, yadda jarirai da kananan yara suke amfani da kayan laturoni na zamani fiye da yadda suke bukata, zai illanta yadda suke mai da hankali kan wani abu da kuma kwarewarsu ta aiwatar da abubuwa , kila zai yi mummunar illa ga makin da za su samu a nan gaba.

Masu nazarin daga cibiyar nazarin ci gaban kananan yara karkashin inuwar jami’ar Harvard sun yi amfani da bayanan da aka gabatar a kasar Singapore ta hanyar bibbiyar kananan yara cikin dogon lokaci, sun tantance alakar da ke tsakanin yadda kwakwalwar kananan yara 437 suke girma da kuma tsawon lokacin da suka dauka wajen yin amfani da kayan laturoni na zamani. Matsakaicin shekarun wadannan yara ya kai 8.84 a duniya yayin da ake bibbiyarsu. An kammala binciken jijjiyoyinsu yayin da shekarunsu suka kai watanni 12 da kuma shekaru 9 da haihuwa. Kana kuma, yayin da shekarunsu suka kai watanni 18 a duniya, an yi binciken kwakwalwarsu. Iyayen wadannan yara sun mika rahoto kan yadda ‘ya’yansu suke amfani da kayan laturoni na zamani. Matsakaicin tsawon lokacin da wadannan yara suka dauka wajen amfani da kayan laturoni yayin da shekarunsu suka kai watanni 12 a duniya ya kai awoyi 2.01 a ko wace rana.

Masu nazarin sun nuna cewa, tsawon lokacin da jarirai suka dauka wajen yin amfani da kayan laturoni na zamani yana karuwa, sai kwarewarsu ta aiwatar da abubuwa yayin da shekarunsu suka kai 9 a duniya ta raunana.

Mutane masu kwarewar aiwatarwa sun gwanance wajen tsara shiri, mai da hankali kan wani abu, rike umurni a ka, da aiwatar da ayyuka a lokaci guda. Irin wannan kwarewa na da matukar muhimmanci wajen kyautata tunani, karatu, samun ilmi, da dai sauransu. Kwarewar aiwatar da abubuwa tana yin tasiri kan nasarorin da mutane suka samu a fannonin zamantakewar al’ummar kasa, ilmi da ayyuka.

Masu nazarin sun yi karin haske da cewa, da wuya jarirai su fahimci wasu bayanai kan fuskar kayan laturoni da dai sauransu. Kuma da kyar su iya  bambanta abun da ke cikin tunaninsu da kuma abu na gaske. Sun bai wa iyaye shawarar kara yin mu’amala da ‘ya’yansu fuska da fuska, a kokarin taimaka musu yin girma, kyautata tunani, a maimakon barin su su yi amfani da kayan laturoni na zamani.

Madam Zhang Chuji, likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, kar a bai wa jarirai ‘yan kasa da watanni 18 a duniya damar yin amfani da kayan laturoni na zamani, illa yin hira ta kafar bidiyo. (Tasallah Yuan)