logo

HAUSA

Xi Ya Taya Erdogan Murnar Sake Lashe Zaben Shugaban Kasar Türkiye

2023-05-29 20:22:09 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga Recep Tayyip Erdogan, bisa sake zabensa da aka yi a matsayin shugaban Türkiye.

Cikin sakon, shugaba Xi ya bayyana cewa, Sin da Türkiye manyan kasashe ne masu tasowa, wadanda ke da muradu iri daya. Kuma a shekarun baya-bayan nan, dangantaka mai muhimmanci dake tsakaninsu ta ci gaba da ingantuwa, haka ma hadin gwiwarsu a bangarori daban-daban ta yi ta samun nasarori.

Ya kara da cewa, yana daukar batun raya dangantakar Sin da Türkiye da muhimmanci, kuma a shirye yake ya hada hannu da shugaba Erdogan wajen fahimta da goyon bayan juna kan batutuwan da ke jan hankalinsu da ma sauran manyan batutuwa, domin ingantawa da ganin dorewar dangantakar Sin da Türkiye cikin aminci. (Fa’iza)