logo

HAUSA

Hukumomin agaji na MDD sun kai kayayyakin agaji yankunan Sudan

2023-05-26 11:19:55 CMG HAUSA

 

MDD da abokan huldarta dake Sudan, sun kai kayayyakin agaji jiya Alhamis, domin isa ga mutanen da za su iya kai wa gare su, a yankunan da ake mutunta yarjejeniyar tsagaita bude wuta.

Ofishin MDD mai kula da ayyukan jinkai (OCHA) ya ce kimanin motocin daukar kaya 20 dauke da kayayyakin da asusun kula da yara na MDD da hukumar kula da masu kaura ta majalisar suka samar ne aka tura sassa daban-daban na Sudan.

Tun a farkon mako hukumomin agajin suka shirya kai kayayyaki, ta yadda motoci 168 za su kai ga mutane sama da miliyan 4 dake fadin kasar, sai dai, yanayin tsaro bai bayar da damar aiwatar da shirin yadda ya kamata ba. Motoci kalilan kadai aka iya turawa domin gudanar da aikin.

Shirin samar da abinci na duniya WFP, ya ce ya samu isa ga sama da mutane 500,000 a jihohi 9 na kasar tun bayan sake fara rabon, kimanin makonni 3 da suka gabata. Shirin na WFP ya kuma shirya raba kayayyakin tallafi a yankin tsakiyar Dafur da jihar Northern.

A ranar Laraba, wasu motoci dauke da kayayyakin abinci na shirin WFP suka isa Wadi Halfa. A yankin Port Sudan kuwa a jiya Alhamis, WFP ya fara samar da abinci ga sabbin ‘yan gudun hijira kimanin 4,000. (Fa’iza Mustapha)