logo

HAUSA

An gudanar da bikin murnar ranar Afirka a birnin Beijing

2023-05-26 11:44:12 CMG Hausa

An gudanar da bikin murnar ranar Afirka a birnin Beijing na kasar Sin jiya Alhamis, inda manyan kusoshi mahalarta taron suka hada da, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar, Qin Gang, da mataimakin firaministan kasar Habasha, Demeke Hassen, da mataimakin firaministan jamhuriyar Demokuradiyar Congo, Christophe Lutundula, da jakadun kasashe daban daban na nahiyar Afirka dake kasar Sin.

Yayin da yake jawabi a wajen bikin, Mista Qin Gang ya ce, Kasar Sin kasa ce mai tasowa mafi girma a duniya, yayin da a nahiyar Afirka aka fi samun kasashe masu tasowa, saboda haka ya kamata a kara karfafa hadin gwiwa tsakanin sassan 2.

Kana Qin ya ba da shawarwari 5 kan yunkurin zurfafa hadin kan Sin da Afirka, wadanda suka hada da, kokarin kare hakkin bangarorin 2, aiwatar da dabarun zamanintarwa da suka dace da su, sa kaimi ga gyare-gyaren tsarin kula da harkokin duniya, kokarin samar da tsaro na bai daya, da kuma karfafa cudanya da koyi da juna tsakanin mabambantan jama’a da al’adu.

A nasu bangare, Demeke Hassen da Christophe Lutundula sun ce, kasashensu na tsayawa kan raya huldar abota da kasar Sin, inda suke neman hadin gwiwa da bangaren Sin a kokarin gaggauta samun ci gaban kasashensu, da gina al’umma mai makomar bai daya ta Afirka da Sin, da ta daukacin dan Adam gaba daya. (Bello Wang)