logo

HAUSA

Shugaba Xi Jinping ya taya murnar bude taron dandalin kimiyya da fasaha

2023-05-26 11:21:31 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika da sakon taya murnar bude taron dandalin kimiyya da fasaha na ZGC a jiya Alhamis, a birnin Beijing na kasar Sin.

Cikin sakonsa, shugaban ya ce, a yanzu haka, ana kokarin gudanar da sabon zagayen juyin juya hali kan kimiyya da fasaha, da inganta tsare-tsaren masana’antu. Sai dai don neman samun ci gaban al’ummu daban daban na bai daya, ana bukatar hadin gwiwar mabambantan kasashe, da matakin bude kofa da more ci gaban da aka samu tare, fiye da yadda ake da wannan bukata a baya. Ya ce kasar Sin a nata bangare, tana tsayawa kan manufar bude kofa, da amfanawa juna, da cin moriya tare, inda take son hada gwiwa da sauran sassan duniya a kokarin kirkiro sabbin fasahohi, da neman ganin ci gaban kimiyya da fasaha ya amfani jama’ar kasashe daban daban.

Shugaban na kasar Sin ya kuma jaddada cewa, ya kamata birnin Beijing na kasar Sin ya yi amfani da fifikonsa a fannonin aikin ilimi, da kimiyya da fasaha, da dimbin kwararru da yake da su, wajen kirkiro sabbin fasahohi, da tsare-tsaren gudanar da harkoki, da ci gaba da gwajin sabbin matakai a unguwar Zhong Guan Cun, inda ake samun dimbin kamfanoni masu fasahohin zamani, da gaggauta gina yankunan kimiyya da fasaha masu inganci , ta yadda za a iya cimma matsayin dake kan gaba a duniya, ta fuskar kirkiro sabbin fasahohi na zamani, da raya masana’antu mai inganci. (Bello Wang)