logo

HAUSA

Sakatariyar AfCFTA ta lashi takobin tabbatar da wadatar abinci a Afrika

2023-05-26 11:36:12 CMG HAUSA

 

Sakatariyar yankin ciniki cikin ‘yanci na Afrika (AfCFTA), ta ce za ta mayar da hankali kan cinikin amfanin gona tsakanin yankunan nahiyar, domin lalubo damarmakin da nahiyar ke da su a bangaren aikin gona da cimma wadatar abinci a nahiyar.

Sakatare janar na sakatariyar Wamkele Mene ne ya bayyana haka a jiya Alhamis, a jawabin da ya gabatar na bude taron dandalin shugabanci na Afrika karo na 7 da aka yi Accra, babban birnin kasar Ghana, inda ya nanata bukatar sauya dokar shigar da abinci nahiyar ta hanyar amfani da dimbin kasar noma da take da su, domin dogora da kanta a fannin samar da abinci.

Wamkele Mene, ya kuma koka cewa, duk da kasancewarta katafariyar damar samar da abinci, har yanzu nahiyar na shigar da abinci daga ketare, inda take bukatar abubuwa kamar hatsi da nama da kayayyakin madara da mai da dangoginsa da sukari, wadanda suka zarce wanda ake samarwa a cikin gida.

Ya kara da cewa, dunkule cinikayyar tsakanin yankuna da ma kasashen nahiyar zai taka muhimmiyar rawa wajen sauya wannan yanayi tare da taimakawa wajen inganta wadatar abinci da dorewarta a nahiyar, yana mai bukatar shugabannin Afrika su gaggauta daukar matakan rushe shingayen dake tsaiko ga cinikayyar amfanin gona a nahiyar da inganta zuba jari a fannin sarrafa amfanin gona da tsarin aikin gona mai jure yanayi. (Fa’iza)