logo

HAUSA

Sin ta musanta zargin leken asiri tare da bayyana Amurka a matsayin wadda ke kan gaba a wannan fage

2023-05-25 21:35:58 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce Sin ta yi watsi da rahoton zargin ta da yin leken asiri da wasu kasashe suka fitar a jiya Laraba, tana mai cewa, rahoton bai yi la’akari da hakikanin hujjoji, da tsarin tabbatar da gaskiya ba.

Da take musanta rahoton na hadakar kasashen Amurka, da Canada, da New Zealand, da Australia da Birtaniya, Mao ta ce ko alama, gwamnatin kasar Sin ba ta umarci wani gungu ya yi kutse cikin na’urorin yanar gizon Amurka ba, don haka zargin, farfaganda ce da yada bayanan jabu da kasashen biyar suka kitsa.

A jiya Laraba ne wasu hukumomin tattara bayanan sirri na kasashen yamma, da hadin gwiwar kamfanin Microsoft, suka fitar da rahoton dake zargin kasar Sin da yin leken asiri, cikin sassa da dama na muhimman na’urorin hukumomin kasar Amurka.

Game da hakan, Mao ta ce sabanin yadda suke yayatawa, kasashen biyar su ne gungun kasashe mafi girma, dake gudanar da ayyukan tattara bayanan sirri, kaza lika hukumar tsaron Amurka ko NSA, ita ce hukumar dake kan gaba a duniya wajen gudanar da kutsen yanar gizo. Don haka abun dariya ne ganin yadda a wannan gaba, sassan biyu suka yi hadin gwiwar fitar da rahoton bogi.  (Saminu Alhassan)