logo

HAUSA

Sin za ta inganta raya dangantakarta da Rasha

2023-05-25 13:17:01 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce a shirye kasarsa take ta hada hannu da Rasha wajen ba tsarin tattaunawar firaministan Sin da na Rasha damar taka rawar da ta dace da aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da inganta ci gaba mai dorewa ta fuskar muhimmiyar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Li Qiang ya bayyana haka ne a jiya Laraba, yayin da yake ganawa da takwaransa na Rasha, Mikhail Mishustin a Beijing.

A nasa bangare, Mikhail Mishustin ya jinjinawa dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha, yana mai cewa, ba tare da la’akari da kalubalen da duniya ke fuskanta ba, Rasha ta shirya hada hannu da Sin wajen aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma da zurfafa hadin gwiwarsu a bangarori daban daban. (Fa’iza Mustapha)