logo

HAUSA

Rikici ya sake barkewa a babban birnin Sudan da kewayensa

2023-05-25 14:11:34 CMG Hausa

Da daren ranar 23 zuwa ranar 24 ga watan bisa gogon wurin, rikici ya sake barkewa tsakanin bangarori masu rikici a Sudan wato dakarun sojin kasar da rundunar ko ta kwana ta RSF, a babban birnin kasar Khartoum da kuma wuraren dake kusa.

Bayan yarjejeniyar tsagaita wuta na wucin gadi da bangarorin biyu suka sanya wa hannu ta fara aiki da yammacin ranar 22 ga wata, yankin Khartoum ya kasance cikin kwanciyar hankali, amma kasa da kwana guda sai aka sake jin amon bindigogi. Wannan zagaye na rikici ya ci gaba da gudana tun daga daren ranar 23 zuwa daren 24 ga wata, kuma ya shafi birnin Khartoum da kewayensa da Arewacin Khartoum da Omdurman. Dakarun sojin Sudan da rundunar ko ta kwana ta RSF sun gwabza fada da juna a sansanonin soja da dama da kuma ginin gidan talabijin na kasar dake birnin Omdurman.(Safiyan Ma)