logo

HAUSA

Za a sake bude reshen kungiyar agaji ta CROISSANT ROUGE ta Qatar a Jamhuriyar Nijar

2023-05-25 08:50:20 CMG Hausa

Kwanan nan shugaban Nijar Mohamed Bazoum ya karbi bakuncin tawagar kungiyar agaji ta CROISSANT ROUGE ta kasar Qatar, a karkashin jagorancin babban magatakardan kungiyar dokta Faisal Mohammed Al-Emadi, makasudin wannan ziyara shi ne sake bude reshen kungiyar ta Qatar da ke Nijar, bayan umurnin rufe shi a shekarar 2018.

Daga birnin Yamai, abokin aikin mu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Ita dai wannan ganawa tare da shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum ta mai da hankali kan batun sake bude da cigaba da gudanar da ayyukan jin kai da kungiyar CROISSANT ROUGE ta Qatar ta saba yi tun yau da ‘yan shekaru a wasu yankunan kasar Nijar, in ji dokta Faisal Mohammed Al-Emadi, bayan ganawar a fadar shugaban kasa da ke nan birnin Yamai. “Mun gamsu sosai da wannan karramawar da shugaban kasar Nijar ya yi mana da sunan dukkan daukacin al’ummar Nijar mai cike da son baki, kuma hakan ya tabbatar mana da cewa mun zo cin nasara domin abin da muka gani da idon mu ya nuna mana cewa shugaban Nijar zai kawo sauki wajen ganin an sake bude reshen mu a wannan kasa mai cike da albarka domin soma gudanar da ayyukanmu kamar yadda muka saba yi tun lokacin farko, kuma ko shakka babu ina ganin nan da ‘yan kwanaki ko makwanni masu zuwa, kome zai daidaita ta fuskar kawo agajin jin kai a kasar Nijar domin jama’a.”

Daga karshen shugaban kungiyar agaji ta CROISSANT ROUGE ta Qatar ya tabbatarwa manema labarai cewa, za su soma fara wasu manyan ayyuka goma sha biyar da suka shafi fannoni daban daban kamar fannin ilimi, fannin tarbiya, da kiwon lafiya, haka kuma da maida hankali kan muhimman ayyuka a bangaren samar da ruwan sha masu tsafta, kuma wadannan ayyuka za su lakume kudaden da suka kai kusan dalar Amurka miliyan bakwai, in ji dokta Faisal Mohammed Al-Emadi.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.