An dawo da aikin hakar danyen mai a yankin tafkin Chadi wanda ake sa ran hako ganga miliyan 732
2023-05-24 11:41:18 CMG Hausa
A jiya Talata 23 ga wata, shugaban Tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin hakar danyen mai na Wadi-B dake Tuba a yankin karamar hukumar Jere a Jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.
Tun dai a 2017 aka dakatar da aikin hakar man a yankin dake Tafkin Chadi sakamakon hare-haren ‘yan kungiyar boko Haram wanda ya tilastawa ma’aikata kauracewa wurin aikin barin yayin da wasu daga cikin su mayakan bokon haram suka hallaka su.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Ana sa ran cikin ‘yan shekaru masu zuwa za a iya hako ganga miliyan 732 na danyen mai, bayan an kammala samun nasarar gina rijiyar.
A lokacin da yake jawabi yayin bikin kaddamar da aikin, shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya yi farin cikin ganin cewa, kafin karewar wa’adin mulkin sa, aka dawo da aikin hakar danyen mai da iskar gas a yankin dake tafkin Chadi.
Ya ce an fara laluben man a yankin tun a 1976, sannan kuma a shekara ta 1985 aka gano iskar gas a yankin na Wadi-B. Inda kuma ya bayyana godiya bisa irin hadin kan da gwamnati da al’ummar jihar ta Borno suka bayar har aka kai ga aka dawo da aikin hakar danyen man.
Shugaba Buhari ya ci gaba da cewa, babu shakka shigowar kamfanin mai na NNPC yankin tafkin Chadi domin hakar mai zai haifar da sakamakon mai kyau, musamman idan aka yi la’akari da nasarorin da kamfanin ya samu wajen hakar danyen mai a Komani dake jihar Bauchi da Ebenyi ta jihar Nasarawa.
Da yake gabatar da jawabin sa, gwamnan jihar Borno Farfessa Babagana Umara Zulum ya ce, wannan aiki shi ne irin sa na biyu da shugaban kasar ya kaddamar a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya bayan na jahohin Bauchi da Gombe. Ya kara da cewa, hakika maido da aikin hakar danyen mai a yankin zai yi mutukar tasiri ga yanayin tattalin arziki da zamantakewar al’ummar jihar ta Borno da ma sauran jihohin dake shiyyar.
Daga bisani Farfesa Babagana Umara Zulum ya ba da tabbacin samun hadin kai da goyon bayan gwamantin jihar ta Borno da al’ummomin jihar wajen samun nasarar kammala aikin hakar danyen man na Wadi-B dake yankin karamar hukumar Jere. (Garba Abdullahi Bagwai)