logo

HAUSA

An yi taro kan taimakawa fararen hula wajen yaki da ta’addanci a Nijar

2023-05-24 11:44:29 CMG Hausa

Ayyukan zaman taro karo na farko kan taimakawa fararen hula wajen yaki da ta’addanci ACLCT sun kammala a makon da ya gabata a zauren taron kasa da kasa na Mahatma Gandhi dake birnin Yamai. Bayan kwanaki uku na musaya, kwararru daban daban, da masu fashin baki da ma kimiyyar yaki da ta’addanci da suka fito daga kasashen Afrika goma da matsalar ta shafa da yammacin duniya sun tattauna kan wannan batu mai sarkakiya na tsaro a yankin Sahel, wannan kuma bisa la’akari da yanayin cikin gida na kasashe.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

A yayin bikin kammala wannan zaman taro, shugaban hukumar karfafa zaman lafiya ta Nijar ta HACP, Janar Abou Tarka Mahamadou ya bayyana farin cikinsa game da shirya irin wannan babban taro a Nijar tare da bayyana muhimmancin maudu’an da aka tattauna kansu. Haduwar ta taimaka wajen fayyace batutuwa da dama na matsalar tsaro a yankin Sahel, dalilai da illolin ta’addanci, rigakafin kaifin kishin addini da dai sauransu.

Yaki da ta’addanci, in ji darekta janar na hukumar barikin kasa, Abdoulaye Haidara, haraka ce ta kowa, kuma dole ta kasance cikin manufa guda. Ya bayyana cewa kwararrun da suka zo sun yi bayani da bada haske kan dukkan hanyoyin da za su taimaka wajen rigakafin ta’addanci, musamman ma salon yin hukunci, na farar hula da na taimakon jama’a. A cewar Haidara, hanyoyi daban daban domin rakiyar shirin su ne kasancewar gwamnati a kowane fanni, kyautata hanyoyin zaman rayuwa da kuma zaman jituwa.

Haka zalika, daya daga cikin muhimman maudu’an wannan zaman taro, a cewar shugabar sashen kare kananan yara da mata, babbar kwamashinar ‘yan sanda Zouera Hassane Haousseize, shi ne salon kusantowa tsakanin fararen hula da jami’an tsaro. Take mai karfin gaske, domin yana taimakawa wajen kafa yarda da taimakon juna tsakanin bangarorin biyu. Kwamishina Zouera, ta jaddada cewa matasa na zama masu hadari wajen kasancewa tare da ’yan ta’adda, ke nan ya zama wajibi a wayar da kansu da ganar da su kan illolin wannan annoba ga al’umma kuma ga makomarsu.

Dukkan shawarwarin da suka biyo bayan wannan zaman taro za su kasancewa matakin farko wajen yaki da ta’addanci.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.