logo

HAUSA

Masanan kasashen ketare sun yaba wa sakamakon da Tibet ta samu a fannonin ci gaba mai inganci da kare hakkin bil’Adama

2023-05-24 10:32:49 CMG Hausa

An gudanar da taron dandalin tattaunawar ci gaban jihar Tibet ta kasar Sin na shekarar 2023 a jiya Talata a birnin Beijing, inda masana fiye da 150 daga kasashe da yankuna 36 sun yi tattaunawa mai zurfi, da musayar sabbin fasahohin inganta hakkin dan Adam ta hanyar samun ci gaba, tare da yaba da sabon ci gaban Tibet a fannonin raya tattalin arziki, da gadon al'adu, da kare muhalli, da hakkin dan Adam da dai sauransu.

Jakadar kasar Mozambique dake kasar Sin, Maria Gustava, ta ce talauci cuta ce dake shafar daukacin bil’Adama, kuma kawar da talauci ba aikin wata kasa ko wani yanki ne shi kadai ba, amma kalubalen duniya ne baki daya da ke bukatar hadin gwiwa. Aikin kau da talauci da raya kauyuka da kasar Sin ta samu a Tibet, ya ba da kwarin gwiwa da jagora mai ma'ana ga kasashe masu tasowa irin su Mozambique wajen kawar da talauci da samar da ci gaba mai dorewa.(Safiyah Ma)