Xi ya amsa wasikar tsoffin masanan dakin adana kayayyakin fasaha na Sin
2023-05-23 13:57:25 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin kuma babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta Sin Xi Jinping ya amsa wasikar tsoffin masana na dakin adana kayayyakin fasahar zane-zane na kasar Sin a ranar 21 ga wannan wata, inda ya bayyana cewa, a yayin da aka cika shekaru 60 da bude dakin, ya mika gaisuwa da taya dukkan ma’aikatan dakin murna.
A cikin wasikar, Xi Jinping ya bayyana cewa, dakin adana kayayyakin fasahar zane-zane na kasar Sin ya shaida nasarorin da sabuwar kasar Sin ta samu a wannan fanni, kana ya yi kirkire-kirkire a fannonin ajiye kayayyaki mafi kyau, da yin bikin nune-nune, da ilimantyar da jama’a a wannan fanni, da yin mu’amala da kasashen waje da sauransu, kuma ya samu nasarori da dama.
A kwanakin baya ne, tsoffin masu fasaha na dakin adana kayayyakin fasahar zane-zane na kasar Sin guda 13 suka rubuta wata wasika ga shugaba Xi Jinping don yin bayani game da bunkasuwar dakin da kuma bayyana imaninsu kan raya sha’anin fasahar zane-zane mai inganci a sabon zamani. (Zainab)