Duniyarmu na bukatar karin gudummowar Sin da kasashen tsakiyar Asiya
2023-05-20 15:24:39 CMG Hausa
An yi nasarar shirya taron kolin shugabannin kasar Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya guda biyar karo na farko a birnin Xi’an na lardin Shaanxi dake arewa maso yammacin kasar Sin jiya Jumma’a 19 ga wannan wata. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi yayin taron, inda ya jaddada cewa, duniyarmu tana bukatar yankin tsakiyar Asiya mai kwanciyar hankali da wadata da zaman jituwa dake cudanyar juna, kana ya gabatar da matakai hudu kan yadda za a gina kyakkyawar makomar Sin da kasashen tsakiyar Asiya ta bai daya, kana ya bayar da shawarwari guda takwas kan hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu, duk wadannan sun samu yabo da amincewa matuka daga shugabannin kasashen yankin mahalartan taron.
Taron ya kasance taron da kasar Sin ta kira a zahiri na farko, tun bayan da ta kulla huldar diplomasiyya da kasashen yankin tsakiyar Asiya, kana shi ne taron koli karo na farko da ta kira tun bayan da aka kafa tsarin hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen tsakiyar Asiya shekaru uku da suka gabata.
A halin yanzu duniyarmu tana fama da manyan sauye-sauye, don haka kasar Sin da kasashe biyar dake yankin tsakiyar Asiya, suna fuskantar jarrabawa mai sarkakiya, kuma dukkansu suna kokarin raya kasashensu, shi ya sa huldar dake tsakaninsu tana kara zurfafa yadda ya kamata. Kamar yadda shugaba Xi ya fada wato gina kyakkyawar makomar Sin da kasashen tsakiyar Asiya ta bai daya, zabi ne mai ma’anar tarihi da suka yi bisa la’akari da babbar moriyar al’ummomin kasashen da makomarsu mai haske. (Jamila)