logo

HAUSA

An fitar da rahoto game da mummunan tasirin salon matsin lamba na diflomasiyyar Amurka

2023-05-19 13:32:10 CMG Hausa

Kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua, ya fitar da rahoto mai taken “Salon Matsin Lamba Na Diflomasiyyar Amurka Da Mummunan Tasirinsa”, wanda ya yi fashin baki game da munanan matakan matsin lamba da Amurka ke aiwatarwa, karkashin diflomasiyyarta ga kasashen duniya.

Rahoton wanda aka fitar a jiya Alhamis, ya kafa hujjoji bisa dalilai, da alkaluma na hakika, ta yadda ya baiwa sassan kasa da kasa zarafin fahimtar salon danniya, da fin karfi dake tattare da diflomasiyyar Amurka, da ma irin mummunar illar da hakan ke yi ga kasashe masu tasowa, da gurgunta yanayin daidaito a shiyyoyi, da zaman lafiyar duniya baki daya.

Kazalika rahoton ya ce Amurka ta saba zargin wasu kasashe da yin amfani da karfin da suke da shi, da aiwatar da siyasar matsin lamba, da matsin tattalin arziki, domin tursasa wasu kasashe na daban bin ra’ayinsu, to sai dai kuma alal hakika, Amurka ce ke aiwatar da diflomasiyyar matsin lamba. 

A yanzu haka, diflomasiyar matsin lamba ce babban makamin da Amurka ke amfani da ita a manufofinta na waje. Kuma tuni kasashe da yawa suka sha fama a hannunta, yayin da kasashe masu tasowa ke kan gaba wajen fuskantar wannan kalubale, baya ga kawayenta da su ma ba su tsira ba.

A cewar rahoton, sassan dake amfani da diflomasiyyar matsin lamba, da kakkaba tukunkumai, da cin zali, da danne sauran kasashe, tare da kawo hargitsi a duniya, daga karshe za su cutar da kansu ne. Don haka, rahoton ke cewa kamata ya yi Amurka ta kawar da wannan tsohon hali nata, na diflomasiyyar matsin lamba, ta komawa adalci, da bin ka’idojin cudanyar kasa da kasa na gaskiya. (Saminu Alhassan)