logo

HAUSA

Ta yaya za a dakile da kandagarkin ciwon zazzabin sauro? (A)

2023-04-04 07:31:15 CMG Hausa

Ranar 25 ga watan Afrilu na ko wace shekara, rana ce ta dakile da kandagarkin ciwon zazzabin sauro ta duniya.

Ciwon zazzabin cizon sauro, mummunan ciwo ne da ke yaduwa tsakanin mutane sakamakon samun kwarin plasmodium a jikin dan Adam. Idan sauro mata masu dauke da kwarin na plasmodium suka ciji mutane, ta haka kwarin ke shiga cikin jikin dan Adam. Hukumar WHO ta yi karin bayani da cewa, akwai kwarin plasmodium nau’o’i guda 5 a duniya wadanda suke sanya mutane kamuwa da ciwon zazzabin cizon sauro, ciki had da wasu 2 mafiya illata ga lafiyar mutane.

Madam Zhang Chuji, likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing. Ta yi karin bayani da cewa, a farkon lokacin kamuwa da ciwon, a kan yi zazzabi, ciwon kai, jin sanyi da dai sauransu, na kwanaki 10 zuwa 15 bayan da sauro ya ciji mutane. Idan ba a ba da magani cikin lokaci ba, to, watakila ciwon zazzabin cizon sauro da kwarin Plasmodium falciparum suka haddasa ya kan yi kamari cikin awoyi 24, har ma ya halaka rayukan mutane.

Ciwon zazzabin cizon sauro ya dade yana illata lafiyar dan Adam a kasa da kasa. Alkaluman hukumar WHO sun bayyana cewa, a shekarar 2020 mutane kimanin miliyan 241 sun kamu da ciwon zazzabin cizon sauro, kana mutane dubu 627 sun rasa rayukansu sakamakon ciwon. A manyan yankuna guda 6 da hukumar WHO ta ware, ciwon ya fi addabar mutanen da ke zama a yankin Afirka, inda yawan masu kamuwa da ciwon ya kai kashi 95 cikin dari bisa jimillar masu kamuwa da ciwon a duniya, kana yawan mamata sakamakon ciwon ya kai kashi 96 cikin dari bisa jimillar mamata a duniya. An kiyasta cewa, yawan kananan yara ‘yan kasa da shekaru 5 da suka mutu sakamakon ciwon zazzabin sauro ya kai kashi 80 cikin dari bisa jimillar mamata a yankin.

Hakika dai, ciwon zazzabin cizon sauro, ciwo ne da ake iya yin rigakafi da kuma shawo kansa. A cikin shekaru 20 da suka wuce, kashe sauro da yin amfani da magunguna masu ruwa da tsaki sun sassauta illolin da ciwon ke haifarwa a duniya. Tun bayan watan Oktoban shekarar 2021 har zuwa yanzu, hukumar WHO ta shawarci yankin Afirka da ke kudu da hamadar Sahara da sauran wuraren da ciwon ya fi yaduwa, da su yi wa kananan yara allurar rigakafin kamuwa da ciwon zazzabin cizon sauro na RTS,S, allura ce ta farko a duniya ta yin rigakafin kamuwa da ciwon. (Tasallah Yuan)