logo

HAUSA

An kaddamar da bikin al’adun Sin da Spaniya don murnar cika shekaru 50 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu

2023-03-30 20:36:43 CMG Hausa

A yau Alhamis ne aka kaddamar da bikin al’adun Sin da Spaniya, don murnar cika shekaru 50 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu, bikin da babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG, da ma’aikatar harkokin al’adu da wasannin motsa jiki ta kasar Spaniya suka karbi bakuncin gudanar da shi tare.

A yayin bikin, shugaban CMG Shen Haixiong, ya bayyana ta kafar bidiyo cewa, daga hanyar siliki zuwa jiragen kasa a tsakanin Sin da Turai, an zurfafa mu’amalar dake tsakanin Sin da Spaniya ta mu’amalar al’adu.

A gun bikin, za a yi amfani da kafar bidiyo don waiwayar tarihin mu’amala a tsakanin Sin da Spaniya, da bunkasuwarsu, da kuma sada zumunta mai zurfi a tsakaninsu a cikin shekaru 50 da suka gabata. Kana za a yi amfani da fasahohin zamani, don yin mu’amala da juna kan zane-zanen kasashen biyu. Har ila yau, za a shaidawa jama’ar kasa da kasa al’adun kasashen biyu, da nasarorin da suka samu daga juna.

Haka zalika kuma, za a watsa labarai don bayyana asalin sada zumunta da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, don bude sabon babi na yin mu’amalar al’adu a tsakanin Sin da Spaniya. (Zainab)