logo

HAUSA

Mai gudanarwa domin Nijar na Bankin Duniya na ziyarar aiki a Nijar

2023-03-30 10:22:55 CMG Hausa

Shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum ya yi wata tattaunawa a ranar jiya 29 ga watan Maris din shekarar 2023 a fadar shugaban kasa da ke birnin Yamai tare da babban jami’i mai gudanarwa domin Nijar na Bankin Duniya, mista Abdoul Salam Bello.

Daga birnin Yamai na jamhuriyar Nijar, wakilinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Shi dai mista Bello ya zo Nijar ne domin sanarwa shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum da shirye shiryen zuwan wata tawaga a Nijar, ta shugaban bankin duniya, mista David Malpass. Kuma, wannan ziyara za ta maida hankali katsokan kan batutuwan karfafa tsaro da zaman lafiya, bunkasuwar tattalin arziki na halartar kowa da dorewa, sannan da batun tsaron abinci, samun makamashi da kuma ilimi.

A cewar Abdoul Salam Bello, wannan ziyara na da muhimmancin gaske domin za ta nuna kyaukyawar huldar dangantaka tsakanin bankin duniya da kasar Nijar, bayan ya fito daga ganawarsa da shugaba Bazoum.

Bankin duniya shi ne abokin huldar cigaba na farko na Nijar, in ji jami’in tare da nuna cewa kasar Nijar ta amfana da tallafi da dama na cikin tsarin matakai daban daban na zuba kudi. Inda a cewarsa bankin duniya na damuwa sosai da bukatun musammun na al’umomin Nijar, kasar da ke yankin Sahel, da ke nesa da ruwan teku, da kuma ta ke fuskantar matsaloli iri daban daban.

Shugaban kasar Nijar, na mai da hankali sosai ga batun ilimin kananan ‘yan mata, kuma bankin duniya na tallafawa Nijar da shugaba Bazoum bisa ga hangensa na cigaban kasa, in ji Abdoul Salam Bello.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai na jamhuriyar Nijar.