logo

HAUSA

Majalissar dokokin tarayyar Najeriya ta amince da bukatar gwamnati na karbo bashi daga bankin raya kasar Sin

2023-03-29 13:37:39 CMG Hausa

A ranar talata 28 ga wata majalissar wakilan Najeriya ta amince da bukatar gwamnatin kasar na ciyo bashin dalar amurka 973,474,971.38 daga bankin raya kasar Sin.

Majalissar ta amince da bukatar ne a zaman ta na jiya talata, bayan kudirin da shugaban kwamatin kasuwanci da dokokin majalisa Abubakar Fulata ya gabatar akan batun.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoton.

Shi dai wannan kudiri yazo ne a dai dai lokacin da yarjejeniyar da tun farko gwamnatin Najeriya ta kulla da bankin Exim na kasar Sin kan batun rancen sama da dala buliyan 22 ya gaza tabbata, duk kuwa da amincewar da majalissar tayi a wancan lokaci.

A sakamakon hakan ne majalissar tayi kwaskwarima ga kudirin yarjejeniyar inda aka sauya mu`amullar zuwa bankin raya kasar Sin.

A lokacin dayake kare wannan kudiri nasa Hon Abubakar Fulata yace tun ainihin shirin karbo bashin da aka kulla da bankin na Exim an kulla shi ne karkashin dokar  karbo rance daga waje na shekara ta 2016-2018, kuma a tsakanin watannin Maris zuwa Yunin 2020 majalissr dattawa data wakilai suka sahalewa gwamnati ta karbo bashin daya zarce dala buliyan 22 karkashin tsarin matsakancin rance daga waje.

Kamar yadda bayanan ma`aikatar kudi ta tarayyar suka nuna za ayi amfani da wadanan kudade ne wajen inganta layin dogo daya tashi daga Kaduna zuwa Kano, aikin da zai gudana karkashin kulawar bankin na EXIM amma daga baya kuma bankin ya janye daga wannan yarjejeniya.

Bayan doguwar muhawara da aka tafka a zauren majalissar wanda wasu wakilai suka nuna kin amincewar su da kulla wata sabuwar yarjejeniyar, amma dai  daga bisani  majalissar ta amince da juyawa kan bankin na raya kasar Sin wanda zai bayar da rancen sama da dala miliyan 973 da za a biya cikin shekaru 15.

Kamfanin gine -gine na kasar Sin CCECC ne zai gudanar da aikin tare da hadin gwiwar ma`aikatar sufuri ta tarayya.

Zaman majalissar na jiya ya gudana ne karkashin jagorancin shugaban majalissar Femi Bajabiamilla.(Garba Abdullahi Bagwai)