logo

HAUSA

Bunkasuwar Sin mai inganci za ta kara samar da damammaki ga kasuwancin waje

2023-03-29 09:58:06 CMG Hausa

Mataimakin firaministan kasar Sin, He Lifeng ya bayyana cewa, bunkasuwar kasar Sin mai inganci, wadda ta ke da nasaba da saurin kirkire-kirkire, da tsarin raya birane da yankuna, da fadada amfani da kayayyaki, da inganta masana’antu, za ta kara samar da damammaki ga harkokin kasuwanci na kasashen waje don samun ci gaba.

He Lifeng ya bayyana haka ne, yayin bikin kaddamar da taron “shekarar zuba jari a kasar Sin”. Yana mai cewa, kasar Sin za ta sa kaimi ga bude kofa ga waje mai inganci, da aiwatar da manufofin tallafi ga kamfanonin ketare, da kuma ci gaba da gina yanayin kasuwanci mai inganci.

Ya kara da cewa, kasar Sin ba za ta sauya manufarta kan zuba jarin waje ba, kuma za ta kara zage damtse wajen jawo masu sha’awar zuba jari a cikin kasar. (Ibrahim)