logo

HAUSA

Sin Za Ta Kara Bude Kofarta Ga Kasashen Waje

2023-03-28 16:48:42 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya jaddada kudurin kasar na dakile hadduran dake tunkarar tattalin arzikin duniya, yayin taron bana na dandalin CDF mai tattauna batutuwan ci gaban kasar Sin.

Kasar Sin ce kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, wadda ke kan gaba wajen cinikayyar kayayyaki da ma hidimomi, baya ga kasancewarta kasuwa mai girma a duniya, wanda ke tabbatar da cewa tana bayar da gagarumar gudunmuwa ga ci gaban tattalin arzikin duniya.

Hakika barkewar annobar COVID-19 da sauransu sun yi mummunan tasiri ga tattalin arzikin duniya, amma duk da haka, gwiwar kasar Sin ba ta yi sanyi ba, inda ta daura damarar ganin farfadowar tattalin arzikin da ma sauran ayyuka da suka jibanci bangaren.

An yi ammana cewa, sabbin manufofin Sin a bana za su taka muhimmiyar rawa wajen farfado da tattalin arzikin kasashe masu tasowa har ma da na duniya baki daya, inda tuni cikin watannin farko na bana, al’amura a cikin gidan kasar ke ta samun tagomashi.

A cewar Firaminsitan, Sin za ta kara bude kofarta ga kasashen waje da kyautata yanayin kasuwa bisa ka’idoji da dokokin kasa da kasa. Bude kofa muhimmiyar manufa ce dake nuna cewa, kasar Sin na maraba da kasashen waje kuma tana goyon bayan samun ci gabansu maimakon neman dakile su. Hakika kasar Sin ta kasance kashin bayan ci gaban duniya, domin har kullum, ita ce mai neman ganin an gudu tare an tsira tare, maimakon neman yin bababkere ko samun ci gaba daga faduwar wani bangare.

An riga an shaida cewa, kariyar cinikayya da sanya haraji fiye da kima ko takunkumai na kashin kai, ba za su amfanawa kowane bangare da komai ba, illa koma baya da rashin kwanciyar hankali.

Ba shakka bude kofar kasar Sin zai kara kwarin gwiwar da kasashen waje da ma ‘yan kasuwarsu da masu zuba jari ke da shi kan kasuwar kasar da karfin tattalin arzikinta da ma gudunmuwar da hakan zai bayar ga habakar na su tattalin arziki, da ma kara cin gajiya daga manufofin kasar Sin da ci gabanta. (Fa’iza Mustapha)