logo

HAUSA

Jami’in Tanzania: Ka’idojin Sin Na Hulda Da Afrika Ka’idoji Ne Na Bai Daya Na Bangarorin Biyu

2023-03-26 16:30:55 CMG Hausa

Mamban majalisar dokokin kasar Tanzania, Vita Kawawa, ya ce ka’idojin kasar Sin na nuna sahihanci da samar da sakamako na hakika da kulla dangantaka da kyakkyakwan fata da kuma jajircewarta wajen ganin an cimma nasara da muradu na bai daya, ba ka’idoji da burin kasar na raya huldarta da kasahen Afrika ba ne kadai, ka’idoji ne na bai daya na bangarorin biyu.

Vita Kawawa wanda kuma shi ne shugaban kwamitin kula da harkokin waje da tsaro na majalisar, ya bayyana haka ne yayin da yake halartar wani taron karawa juna sani domin cika shekaru 10 da ziyarar da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya kai kasar da kuma kafuwar wadancan ka’idoji. 

A cewarsa, karkashin wadancan ka’idoji da jajircewa, Sin da Tanzania, sun gudanar da hadin gwiwa mai amfani da samar da moriyar ta zahiri ga Tanzania. Ya kuma bayyana fatan ganin dangantakar kasashen biyu ta kara samun babban ci gaba da samar da moriya ga al’ummominsu. (Fa’iza Mustapha)