logo

HAUSA

Wang Yi: Ya kamata daidaita rikicin Ukraine a siyasance ya zama yarjejeniya tsakanin Sin da Turai

2023-03-24 16:13:50 CMG HAUSA

 

Darektan ofishin kula da harkokin waje na kwamitin kolin JKS, Wang Yi, ya tattauna ta wayar tarho da Emmanuel Bonne, mai baiwa shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron shawara kan harkokin diflomasiyya, bisa bukatar Bonne.

Wang ya yi wa Bonne karin bayani kan ziyarar da shugaba Xi Jinping ya kai kasar Rasha, inda ya ce wannan ziyara ce mai muhimmanci tsakanin manyan kasashen biyu, kuma ziyarar ba kawai ta hadin gwiwa kadai ba ce, amma har ma ta zaman lafiya.

Wang ya kara da cewa, kasar Sin na ci gaba da tsayawa tsayin daka, wajen yayata shawarwarin zaman lafiya kan batun Ukraine. Wang ya bayyana cewa, bangaren Sin na fatan kasar Faransa da sauran kasashen Turai, su ma za su taka rawar da ta dace a wannan fanni. Yana mai cewa, ya kamata tsagaita bude wuta, da maido da tattaunawar zaman lafiya da sasanta rikicin a siyasance su kasance yarjejeniya bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Turai.

A nasa bangaren kuwa, Bonne ya bayyana jin dadinsa kan rawar da kasar Sin ta taka, wajen inganta shawarwarin zaman lafiya. (Ibrahim)