logo

HAUSA

UNECA: Kasashen Afirka guda 10 na fuskantar matsanancin talauci

2023-03-23 10:55:34 CMG Hausa

Mataimakiyar babban sakataren hukumar kula da tattalin arzikin Afirka ta MDD (UNECA) Hanan Morsy ta bayyana cewa, kasashe 10 na Afirka sun fuskanci matsanancin talauci a nahiyar.

Mosry ta shaidawa taron ministocin kudi, tsare-tsare da raya tattalin arzikin Afirka karo na 55 na hukumar da aka gudanar ranar Talata a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha cewa, kasashen Burundi, da Somaliya, da Madagascar, da Sudan ta Kudu, da Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, da Malawi, da Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, da Guinea-Bissau, da Mozambique da Zambia, su ne kasashen da suka fi fuskantar matsalar talauci a nahiyar Afirka.

Da take karin haske kan wani binciken da hukumar ta UNECA ta gudanar kuwa, Morsy ta ce a cikin wadannnan kasashe 10, tsakanin kashi 60 zuwa kashi 82 na al'ummar kasashen matalauta ne.

A dangane da binciken, Morsy ta ce, hukumar UNECA ta kiyasta cewa, magidanta a Afirka suna kashe kashi 40 cikin 100 na abin da suke samu a kan abinci, kuma tasirin rikice-rikicen dake faruwa a sassa duniya, ya shafi magidanta mafiya fama da talauci a Afirka matuka. (Ibrahim Yaya)