Xi da Putin sun amince su zurfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a sabon zamani
2023-03-22 10:54:04 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a fadar Kremlin dake birnin Moscow jiya Talata, inda suka yi tattaunawa ta gaskiya, sada zumunci mai fa’ida kan alakar da ke tsakanin kasashen biyu, da manyan batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya, da suka shafi moriyar juna, sun kuma cimma sabbin fahimtar juna masu muhimmanci a fannoni da dama.
Bangarorin biyu sun amince da martaba ka'idojin makwabtaka, da abokantaka da hadin gwiwa tare da samun nasara wajen ciyar da mu'amala da hadin gwiwa a fannoni daban daban, da zurfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a sabon zamani.
Xi da Putin sun yi imanin cewa, mu'amalar da ke tsakanin bangarorin biyu a yayin ziyarar, tana da zurfi, mai kuma cike da wadata, ta kuma sanya wani sabon kuzari ga ci gaban hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Rasha a sabon zamani.
Bayan shawarwarin, shugabannin biyu sun rattaba hannu kan wata sanarwar hadin gwiwa ta jamhuriyar jama'ar kasar Sin da tarayyar Rasha, kan zurfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a sabon zamani da kuma sanarwar hadin gwiwa na shugaban kasar Sin da na shugaban Tarayyar Rasha, kan shirin raya kasa nan da shekarar 2030 kan abubuwan da suka sanya a gaba a hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin kasashen Sin da Rasha.
A yayin ziyarar, bangarorin biyu sun rattaba hannu kan takardun hadin gwiwa a fannonin aikin gona, da dazuka, da binciken kimiyya da fasaha, da ka'idojin kasuwanci, da kafofin watsa labarai. (Ibrahim Yaya)