logo

HAUSA

Shugaban tarayyar Najeriya ya kaddamar da cibiyar yaki da ta`addanci ta kasa a birnin Abuja

2023-03-22 09:41:48 CMG Hausa

A ranar Talata 21 ga watan, shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabon ofishin mai ba shi shawara kan harkokin tsaro da kuma cibiyoyi biyu na yaki da ta’addanci na kasa a birnin Abuja.

Cibiyoyin biyu da aka samar musu da kayyakin aiki na zamani za su taimakawa kokarin da ake yi na magance matsalolin tsaro a kasar musamman  ayyukan ta’addanci da yakar masu tsastauran ra’ayi.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

A lokacin da yake jawabi wajen kaddamar da cibiyoyin biyu dake da babban matsayi na duniya, shugaba Muhammadu Buhari ya ce cibiyoyin za su kasance cikin manyan ayyuka abin tunawa da shi bayan ya bar ofis, kuma za su taimakawa gwamnati mai zuwa wajen daidaita ayyukan tsaro da yaki da ta’addanci kamar yadda ya kamata.

Shugaban wanda ya yi amfani da wannan dama wajen bayyana muhimman abubuwan da gwamnatinsa ta cimma kan tsaron kasa, wanda suka hadar da yaki da ta’addanci, ’yan fashi da makami, masu garkuwa da mutane, da masu fafutukar a-ware, da masu satar danyen mai, da masu satar fasaha da kuma tsagerun yankin kudu maso kudu.

Ya ci gaba da cewa gagarumar nasarar da gwamnatinsa ta samu wajen maido da zaman lafiya a yankin arewa masu gabas abin alfahari ne sosai, wanda kafin zuwansa ’yan ta’adda sun mamaye yankuna da dama tare da tilastawa jama’a bari muhallansu, amma yanzu kowa yana komawa gida ba tare da nuna wata fargaba ba.

Shugaba Buhari ya ce an samu nasarar hakan ne bisa jajircewar sojoji da sauran jami’an tsaron kasar tare kuma da tallafin bangarorin tsaron hadin gwiwa na kasa da kasa.

Ya kuma yi fatan wadannan cibiyoyi guda biyu musamman na yaki da ta’addanci da aka kaddamar, wadanda kuma aka samar musu da kayayykin aiki na zamani za su kara taimakawa matuka kan sha’anin tsaro ba wai kawai a Najeriya ba, har ma ga sauran kasashe dake yankin tafkin Chadi.

A nasa jawabin, mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro Major Janaral Babagana Monguno mai ritaya wanda ofishinsa ne ya dauki ragamar samar da cibiyoyin, ya ce yanayin tsaro na duniya da na cikin gida a shekaru 30 da suka gabata, shi ne ya tilastawa ofishin nasa yin gyare-gyare a harkar tsaro tare kuma da fadada wasu ayyukan da suke da nasaba da tsaron kasa.

Janar Mongono har’ila yau, ya kara da cewa cibiyoyin za su kara habaka irin gudumawar da Najeriya ke bayarwa a manufofin yaki da ta’adanci a duniya.

Ya kuma yabawa shugaban kasar saboda cikakkkiyar damar da ya ba shi har ta kai shi ga kammala aikin samar da wadannan cibiyoyi biyu.

A jawabinsa babban jami’in majalissar dinkin duniya a Najeriya Matthias Schmale wanda ya samu wakilcin Kimaris Toogood yabawa ya yi da ci gaba da sojojin Najeriya suka samu na rage karfin ayyukan kungiyar IS dake yammacin Afrika da kuma kungiyar Boko Haram. Ya kuma kara jaddada kudirin Majalissar dinkin duniya wajen taimakawa Najeriya ta fuskar tsaro da gina kasa. (Garba Abdullahi Bagwai)