logo

HAUSA

An sako yan kasashen yammacin duniya biyu da kungiyar JNIM ta yi garkuwa dasu

2023-03-22 09:46:15 CMG Hausa

A yammacin ranar Litinin 20 ga watan Maris din shekarar 2023, hukumomin kasar Nijar suka bada labarin sakin ’yan kasashen yammacin duniya biyu da ke hannun kungiyar Jama’at Nusral Islam Walmusulmin JNIM, su ne da kasar Faransa Olivier Dubois da Jeffrey Woodke dan kasar Amurka bayan sun shafe watanni da watanni kungiyar ’yan ta’adda ta JNIM tana garkuwa da su.

Wakilinmu daga birnin Yamai, Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

A gaban manyan jami’an gwamnatin Nijar da na ofishin jakadancin Faransa a Nijar da na ofishin jakadancin Amurka a Nijar ne, ministan cikin gidan kasar Nijar, ya ba da sanarwar sako Olivier Dubois dan asalin kasar Faransa, kuma dan jarida da aka sace a ranar 8 ga watan Afrilun shekarar 2021 a garin Gao na kasar Mali, da shi kuma dan asalin kasar Amurka Jeffrey Woodke da aka sace shi a ranar 14 ga watan Oktoban shekarar 2016 a garin Abalak na yankin Tahoua a Nijar, mista Woodke ya jima a kasar Nijar yau fiye da shekaru 30, kuma shi ne shugaban kungiyar kasa da kasa ta matasa da yarinta da bakuncin haure da ci gaba. A cewar ministan cikin gidan Nijar, wadannan mutane biyu da aka yi garkuwa da su, hukumomin kasar Nijar sun karbo su cikin koshin lafiya, kafin daga bisani aka mika su bi da bi ga hukumomin kasar Faransa da na Amurka. A lokacin da suke bayani gaban ’yan jarida, Olivier Dubois da Jeffrey Woodke, sun bayyana godiyarsu ga hukumomin Nijar da ba su yi kasa a gwiwa ba domin ganinsu sun samu walwala, da kuma bayyana godiya ga kasashensu bisa nacewar da shugabannin kasashensu suka yi wajen an sako su ba tare da biyan kudin fansa ba. Inda daga karshe jakadan kasar Faransa a Nijar tare da takwaransa na kasar Amurka a Nijar suka bayyana gamsuwarsu bisa ga kokarin da hukumomin Nijar suka yi, a sahun gaba shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum wajen ganin kungiyar Jama’at Nusral Islam Walmusulmin JNIM ta sako ’yan kasarsu da ta yi garkuwa da su a tsawon watanni dama.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.