logo

HAUSA

Sin ta amsa tambayoyi game da harin da aka kaiwa kamfanin Sin dake Afirka ta tsakiya

2023-03-20 15:46:37 CMG HAUSA

 

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya bayyana a gun taron manema labarai cewa, an kaiwa wani kamfani mai zaman kansa na Sinawa hari a jiya Lahadi a Afirka ta tsakiya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar Sinawa 9, yayin da wasu 2 suka ji munanan raunuka. Jami’in ya ce shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mai da hankali sosai kan lamarin, tare da ba da umurni cewa, dole ne a ba da jiyya bisa iyakacin kokari ga wadanda suka ji raunuka, da kula da harkokin da suka jibanci batun a nan gaba, da kuma gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban kotu yadda ya kamata, don tabbatar da kwanciyar hankali da zaman rayuwar Sinawa a wurin. (Amina Xu)