logo

HAUSA

Matashin HK ya bayyana kwarin gwiwa kan kwanciyar hankalin yankin a taron MDD

2023-03-18 20:19:34 CMG Hausa

A jiya Jumma’a 17 ga watan Maris, Yang Zhenglong, wani matashi daga yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, kuma mamba a kungiyar MDD ta kasar Sin, ya yi jawabi a yayin taron kwamitin kare hakkin bil Adama na MDD karo na 52, inda ya bayyana cikakken amincewa da kwanciyar hankali da ci gaban Hong Kong na dogon lokaci

Yang Zhenglong ya bayyana cewa, Hong Kong birni ne na musamman kuma mai karfin gaske, kuma manufar nan ta “kasa daya, amma tsarin mulki iri biyu” ta baiwa Hong Kong damar cin gashin kanta sosai. Haka kuma aiwatar da dokar tsaron Hong Kong ta tabbatar da kwanciyar hankali da tsaro a yankin tare da samar da kasa mai albarka don ci gaban tattalin arzikin yankin. (Ibrahim)