logo

HAUSA

Wani dan sanda daga jihar Xinjiang ya fadawa kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD yadda yake ji

2023-03-18 16:29:08 CMG Hausa

Wani dan sanda daga jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta dake kasar Sin, mai suna Waresijiang Maimaiti, ya shaidawa zaman taron kwamitin kare hakkin dan-Adam na MDD karo na 52, yadda ransa ke baci a duk lokacin da ya tuna da ta'addancin da ya taba fuskanta.

Waresijiang Maimaiti, wanda ya shafe shekaru 13 yana aiki a ofishin 'yan sanda dake garin Otbeshi na gundumar Wushi ta lardin Aksu na jihar Xinjiang, ya shaidawa majalisar cewa, a matsayinsa na dan sanda, a yayin da yake aikin shawo kan ta'addanci daban-daban a shekarun baya, ya shaida yadda mutane da dama da ba su san hawa ba balle sauka suka rasa rayukansu, da hasarar dukiya mai tarin yawa da aka yi, da kuma mummunar barna ga zaman lafiyar al’umma da kuma haifar da wahala mai tsanani ga ‘yan kabilu daban-daban.

Ya bayyana cewa, ta'addanci barazana ne ga daukacin bil-Adama, kuma 'yan ta'adda makiyi ne na kowa da kowa, kuma yaki da ta'addanci da dokokin jihar Xinjiang masu nasaba da dakile laifuka, wani mataki ne na adalci kan tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama'a, da kiyaye zaman lafiyar jama'a da kare hakkin bil-Adama.

Ya jaddada cewa, ba tare da nuna wata kabila ba,ko nuna wani bambanci ba, kokarin da Xinjiang ke yi na kawar da tsattsauran ra'ayi, ya kasance wani muhimmin mataki na kare da hukunta masu tsattsauran ra'ayi da kuma dakile ayyukan ta'addanci. (Ibrahim)