logo

HAUSA

Sakatariyar baitul’malin Amurka: kila za a fuskanci matsalar karbar kudi daga banki idan matsalar kudi ta kara tsananta

2023-03-17 14:47:38 CMG Hausa

Jiya Alhamis ne, sakatariyar baitul’malin Amurka Janet Yellen ta bayyana cewa, yadda bakunan Silicon Balley Bank da Signature Bank suka durkushe, ya jijjiga kasuwar hada-hadar kudi. Domin magance kara tsanantar wannan yanayin da ake ciki, hukumomin sanya ido kan harkokin hada-hadar kudi na Amurka, sun dauki matakai don gaggauta tallafawa bankunan biyu, a kokarin tabbatar da tsaron dukiyoyin masu ajiya.

Sakatariya Yellen ta yi wannan bayani ne, zaman da kwamitin kudi na majalisar dattijai ya kira cewa, rufe bankin na Silicon Valley da bankin Signature ya haifar da rudani a kasuwa, inda ta kara da cewa, matakin gaggawar da hukumar ta dauka kan bankunan biyu ba ya nufin cewa wannan shi ne ka'ida ta gaba, kuma gwamnatin Amurka ba za ta ba da tabbaci kan wani ajiya na bankuna ba. Ta kuma yi gargadin cewa, hakan na iya haddasa matsalar karin karbar kudi daga banki idan matsalar ta kara tsananta.

Kafofin yada labaran Amurka sun bayyana cewa, jiya Alhamis wasu manyan bankunan Amurka da suka hada da Goldman Sachs da Morgan Stanley, sun zuba dalar Amurka biliyan 30 a bankin First Republic. (Kande Gao)