logo

HAUSA

Sin na fatan farfadowar dangantakar diflomasiyyar Saudiyya da Iran za ta taimaka ga kyautata halin da ake ciki a Yemen

2023-03-16 13:22:55 CMG Hausa

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake Majalisar Dinkin Duniya, Geng Shuang ya yi jawabi a wajen taron da kwamitin tsaron majalisar ya shirya game da batun kasar Yemen, inda yake sa ran nasarorin da aka samu a wajen shawarwarin da tawagogin kasashen Saudiyya da Iran suka gudanar a Beijing, za su kirkiro yanayi mai kyau ga daidaita halin da ake ciki a Yemen.

Geng ya ce, halin tsaro da Yemen take ciki na fuskantar babbar matsala yanzu, inda ake samun musanyar wuta a wasu sassan kasar. Kasar Sin ta yi kira ga bangarori daban-daban da su yi hakuri da kasancewa cikin nitsuwa, da kaucewa daukar matakan da ka iya haifar da tashe-tashen hankalu. Kana, Sin ta yi kira ga kasa da kasa da su kara tallafawa Yemen, da samar da cikakken tabbacin kudi ga MDD don ta dauki matakai a Yemen.

Geng ya kara da cewa, an cimma tudun-dafawa a gun shawarwarin da aka gudanar tsakanin tawagogin Saudiyya da Iran a makon jiya a Beijing, inda suka sanar da farfado da alakar jakadancinsu, nasarar da za ta taimaka matuka ga shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali da kara hada kawuna a wannan shiyya, gami da sa ran cewa, za ta taimaka ga kirkiro kyakkyawan yanayi ga kyautatuwar halin da Yemen take ciki. Kasar Sin tana son hada kai tare da sauran kasashe, don ci gaba da daidaita matsalar Yemen, da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya. (Murtala Zhang)