logo

HAUSA

Ma’aikatun ruwa da na ilimi a tarayyar Najeriya sun kulla yarjejeniyar fahimta kan samar da tsaftataccen ruwa a makarantu

2023-03-16 09:17:00 CMG Hausa

A ranar Laraba 15 ga wata, ma’aikatar albarkatun ruwan sha da takwararta ta ilimi a tarayyar Najeriya suka sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna wajen samar da tsaftataccen ruwan sha da muhalli a harabobin manyan makarantun kasar.

Sun sanya hannu ne karkashin shirin hukumomin UNICEF da WHO na samar da ruwan sha da muhalli mai tsafta ga al’ummar kasar don tabbatar da dorewar ci gaba na muradun karni SDG.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Da yake jawabi jim kadan bayan sanya hannu kan yarjejeniyar, ministan albarkatun ruwa na tarayyar Najeriya Engr. Sulaiman Adamu ya ce, an samar da shirin ne a makarantun gwamnatin tarayya karkashin yarjejeniyar hadin gwiwa domin tabbatar da ganin cewa dalibai sun wadatu da ruwa mai kyau tare kuma da rayuwa cikin muhalli mai inganci.

Engr. Abdullahi Adamu ya ci gaba da cewa, ma’aikatarsa ta himmatu sosai wajen kulla makamanciyar wannan alaka da wasu hukumomi na daban don ganin cewa an kai ga cimma burin muradun karni nan da 2030.

Ya ce za a iya cimma wannan buri ne cikin gaggawa muddin aka samu sadaukar da kai a tsakanin gwamnati, kungiyoyin al’umma, kamfanoni da hukumomi masu zaman kansu, sarakuna da kuma cibiyoyin yada addini kana da sauran jama’a.

Ministan ruwan na tarayyar Najeriya ya kuma kara dacewa, “Mun kulla irin wannan yarjejeniya da cibiyoyin kiwon lafiya, kuma muna kokarin yin hakan da hukumar lura da masu yiwa kasa hidima ta kasa, a takaice dai muna da wannan shiri na tsafta ruwa da muhalli a fagen ilimi, kiwon lafiya da kuma a tsakanin matasa duk dai a kokarin samun nasarar shirin dorewar muradun karni na MDD.”

Engr. Abdullahi Adamu ya ce a yanzu haka ma’aikatarsa ta samar da duk kudaden da ake bukata wajen gudanawar da Shirin cikin kasafin kudi na 2023, kuma akwai yakinin cewa nan da 2030 shirin zai karade dukkan makarantun kasar. 

A nasa jawabin, ministan ilimi na tarayyar Najeriya Adamu Adamu farin cikinsa ya bayyana bisa wannan yarjejeniya da aka kulla tsakanin ma’aikatarsa da ma’aikatar albarkatun ruwa, inda ya yi fatan cewa irin nasarar da ma’aikatar ruwa ta samu wajen samar da ban dakuna a wuraren mu’amullar jama’a za a sami makamancin hakan a karkashin wannan shiri na inganta muhalli da ruwan sha.

“Muddin dai ba a samu tsaftattaccen ruwa sha da ingantaccen muhalli a makarantun mu ba, zai yi wahala a sami wani sakamakon a zo a gani daga makarantun, tsafta tana da matukar mahimmanci wajen samun ilimi mai inganci.” (Garba Abdullahi Bagwai)