logo

HAUSA

Wakilin Sin ya bayyana rashin gamsuwa da yadda Amurka ta gabatar da daftarin kudurin kwamitin sulhu kan Sudan ta Kudu

2023-03-16 19:26:20 CMG Hausa

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Dai Bing, ya yi bayani bayan da kwamitin sulhun ya kada kuri’a kan tsawaita wa’adin aikin wanzar da zaman lafiya na MDD a Sudan ta Kudu jiya Talata, inda ya nuna rashin gamsuwa da ayyukan da Amurka ta yi a matsayin wadda ta rubuta daftarin kudurin.

Ya ce, abin takaici ne yadda wasu daga cikin abubuwan da ke cikin daftarin kudurin da kwamitin sulhun ya kada kuri’a ba tare da wani bangare sun matsa lamba kan Sudan ta Kudu ba, kuma wa’adin da aka bai wa tawagar MDD a Sudan ta Kudu, bai yi la’akari da hakikanin halin da ake ciki ba, wanda ya dagula da muradun siyasar wasu kasashe. Don haka, dole ne kasar Sin ta kaurace wa kada kuri’ar.

Ya bayyana cewa, ya kamata kasashen duniya su kalli matakin ci gaban Sudan ta Kudu da idon basira da matsaloli da kalubalen da take fuskanta, wajen inganta harkokin mulkin kasa, tare da baiwa Sudan ta Kudu hakuri da ma kwarin gwiwa. Sai dai kuma, daftarin kudurin yana da tsauri da kuma rashin daidaito. Batutuwa kamar zabe, da batun kudi, kula da albarkatun kasa da sauran batutuwa, al’amura na cikin gida a kowace kasa. Daftarin kudurin, ba tare da amincewar kasar Sudan ta Kudu ba, ya gabatar da bukatu da sharudda kan wadannan batutuwa, wadanda ko shakka babu, sun zarce iyakokin da aka saba. (Ibrahim)